Iran  Ta Yi Wa Lebanon Tayin Taimaka Ma Ta  Da Kayin Aiki  Bayan Harin Da HKI Ta Kai Wa Kasar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa a shirye take ta bayar da kayan aiki na bincike ga kasar Lebanon domin gano hakikanin abinda ya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa a shirye take ta bayar da kayan aiki na bincike ga kasar Lebanon domin gano hakikanin abinda ya faru.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a tsakanin ministan harkokin waje Abbas Araqci da na kiwon Lafiya Muhammad Ridha Zafarkandi  na Iran da  takwarorinsu na Lebanon sun bayyana cewa kasar tasu a shirye take ta bayar da kayan aiki ga Lebanon domin gano hakikanin abinda ya faru.

Dukkanin ministocin biyu na Iran sun yi tir da hari na HKI tare da nuna alhininsu ga gwamnati da kuma al’ummar Lebanon.

Har ila yau ministan harkokin wajen Iran ya yi godiya ga takwaransa na Lebanon Abdullahi Bu Habib akan gaggauta kula da jakadan Iran a Lebaon, Mujtaba Amani da kai shi asibiti bayan da ya sami rauni sanadiyyar fashewar na’urorin sadarwar.

Tun da fari kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Nasir Kan’ani ya yi tir da harin na HKI ta hanyar na’urorin sandarwa, tare da bayyana shi a matsayin kisan kiyashi.

Har ila yau kakanin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce, harin ta’addancin da HKI ta kai cigaba ne da keta dokokin kasa da kasa da kuma take hakkokin bil’adama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments