Iran ta yi Allah wadai da hukuncin da wata kotu a Amurka ta yanke wanda ya haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da kuma yajin aiki, tana mai cewa a fili hukuncin ya keta ‘yancin fadin albarkacin baki.
A wani sako a shafinsa na ‘’X’’, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kan’ani ya yi Allah wadai da hukuncin da alkalin ya yanke wanda ya tilastawa dubban ma’aikatan jami’ar California dakatar da yajin aikin da suke yi tare da komawa bakin aikinsu ranar Litinin.
Ana dai yin zanga-zangar ne a jami’o’i guda shida don nuna adawa da martanin hukumomin kasar game da zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Mista Kan’ani ya ce “Jami’an kungiyar daliban Jami’ar California sun yi imanin cewa umarnin da kotu ta bayar na dakatar da yajin aikin da dalibai da ma’aikatan jami’o’in ke yi na goyon bayan Falasdinu ba shi da amfani.”