Iran, Ta Yi Tir Da Harin Ta’addancin Da Ya Afku A Omman Yayin Zaman Makokin Imam Hussain (AS)

Iaran ta yi da allawadai da harin ta’addancin da ya auku kan masu zaman makokin Imam Hussain (AS), a binrin Muscat na masarautar Omman. Kakakin

Iaran ta yi da allawadai da harin ta’addancin da ya auku kan masu zaman makokin Imam Hussain (AS), a binrin Muscat na masarautar Omman.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ne Nasser Kanani ya bayyana yin Allah wadai na kasar da harin ta’addancin da ya afku a daren jiya a lokacin zaman makokin Imam Hussain (AS) a birnin Muscat, inda mutane hudu suka yi shahada.

Mista Kanani ya bayyana goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga gwamnati da al’ummar masarautar Oman dangane da ayyukan ta’addanci da rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi fatan Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a wannan ta’adi tare da jajantawa iyalansu.

Ƴan sanda a kasar ta Oman dai sun ce akalla mutum hudu ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a harin da aka kai masallacin Wadi al-Kabir da ke kusa da babban birnin kasar Muscat.

Hotunan da aka yada a intenet sun nuna yadda mutane ke ƙoƙarin tserewa daga masallacin da aka bude wa wuta, a lamarin da ba a cika samun irinsa a Oman ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments