Iran ta kakkausar suka tare da yin fatali da sanarwar bayantaron taron hadin guiwar kungiyar tarayyar Turai EU, da kuma ta hadin kan kasashen yankin tekun Fasha, (EU-GCC).
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ne ya yi kakkausar sukan kan sanarwar da ya alakanta da ‘’tsoma baki’’ kan harkokin cikin gida na Iran.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, bayan taron ya fito da sanarwar da ta zargi Jamhuriyar Musulunci ta Iran da “mamaye” tsibiran Iran guda uku na tunb karama da babba da Abu Musa inda sukayi ikirarin cewa tsibiran na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ne.
Ministan harkokin wajen kasar ya ce, “Tsibiran guda uku na Iran ne, kuma za su ci gaba da kasancewa a haka har abada.”