JMI ta bayyana cewa zata yi amafani da hakkinta wanda doka ya bata na ficewa daga yarjeniyar NPT don sake farfado da takunkuman tattalin arziki na MDD a kan kasar.
Jakadan kasar Iran a MDD, Amir Saeid Iravani ne ya bayyana haka a jiya Laraba.
Kamfanin dillanbcin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a wata wasika da ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD a jiya. Ya kuma kara da cewa Iran zata yi amfani da dokokin da suka bada damar yin hakan.
Kasashen Turai guda Uku jamusa Farana da Burtania suna son su yi amfani da damar da ake kira snap back don sake farfado da takunkuman MDD a kan kasar na yarjeniyar JCPOA.
Ya kammala da cewa yarjeniyar JCPOA bata da amfanmi bayan da suka kauracewa yin aiki da ita na shekaru.