Iran, Ta Yi Gargadi Game Da Yadda Wasu Kasashe Ke Amfani Da IAEA Domin Cimma Manufofinsu Na Siyasa

Iran, ta yi gargadi game da yadda wasu kasashe ke amfani da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya domin cimma manufofinsu na Siyasa. Da

Iran, ta yi gargadi game da yadda wasu kasashe ke amfani da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya domin cimma manufofinsu na Siyasa.

Da yake bayyana hakan a wani taron manema labarai na mako mako, ministan harkokin wajen kasar na riko Ali Bagheri Kani, ya bayyana cewa, yadda wasu kasashe mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar ta IAEA ke amfani da ita wajen cimma manufofinsu na siyasa, yana da illa ga hukumar.

Kallama nasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen (Birtaniya, Faransa, da kuma Jamus) ke matsin lamba ga hukumar ta IAEA, kan ta fitar da wani kuduri kan shirin nukiliyar Iran.

Idan har aka zartar da kudurin, to tamakar wani kuskure ne da babu makawa zai haifar da takun-tsaka, inji shi.

Iran da manyan kasashen duniya sun cimma yarjejeniya nukiliya a shekarar 2015, wadda a karkashinta Teheran ta jingine wani bangare na shirinta na nukiliya, yayin da aka cire mata takunkumin da aka kakaba mata na tattalin arzikin Iran.

To saidai, Tehran ta fara dakatar da wasu daga cikin al’kawulan data dauka a karkashin yarjejeniyar a shekarar 2019, shekara guda bayan gwamnatin Amurka karkashin tsohon shugaba Donald Trump, ta yi watsi da yarjejeniyar tare da mayar da takunkumi kan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments