Wakilin Iran a MDD Amir Sa’id Ir Afati, ya jaddada halarcin harin da Iran ta kai wa HKI a karo na biyu, mai suna: “Wa’addusadiq 2” domin HKI ta yi furuci a cikin wauta da cewa ita ce ta kashe Shahid Isma’ila Haniyya a birnin Tehran.
Wakilin na Iran a MDD ya ce; Wannan shi ne karo na farko da HKI take yin furuci a cikin wauta da daukar nauyin aikata mummunan laifi.
Ir Afati wanda ya rubuta wasika zuwa babban magatakardar MDD, Antonio Gutrres da a ciki ya bayyana masa cewa; Wannan furucin da ‘yan mamaya su ka yi, yana sake tabbatar da laharci martanin da Iran din ta kai a ranar 1 ga watan Oktoba 2024, da kuma dacewarsa da doka.
Haka nan kuma ya tabbatar da matsayar Iran na cewa; ‘tsarin mamaya na Isra’ila, na ta’addanci ne wanda kuma yake a matsayin barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaronta.
Wannan dai yana zuwa ne bayan da ministan yakin HKI “Yisra’il Katz’ ya yi furta cewa su ne su ka kashe Isma’ila Haniyyah a cikin birnin Tehran, da hakan yake nufin da cewa; Isra’ila ce ta kashe shi”.
Ministan yakin na HKI ya fadi haka ne a lokacin da yake yi wa Ansarullah ta Yemen barazana, yana cewa, za su kashe su kamar yadda su ka kashe Isma’ila Haniyya a Tehran, Sinwar a Gaza da kuma Sayyid Nasrallah a Lebanon.