Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah-wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na ayyana sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin mutum maras nagarta.
Esmaeil Baghaei ya ce a safiyar Juma’a cewa, matakin na da nufin muzgunawa Antonio Guterres tare da tilasta masa yin shiru kan laifukan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kakakin ya kara da cewa Isra’ila ita ce gwamnatin da tsohon jakadanta ya yaga takardar yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya a gaban duniya baki daya.
Baghaei ya kara da cewa, firaministan Isra’ila ya kuma yi amfani da dandalin taron Majalisar Dinkin Duniya don rufe baki kasashen duniya ta hanyar yin barazanar haifar da karin kisan jama’a mata da kananan yara a Gaza da Lebanon.
A ranar Laraba, Isra’ila ta ayyana Guterres a matsayin mutum maras nagarta wanda ba a da bukatarsa, inda ta zarge shi da gaza yin Allah wadai da harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan gwamnatin yahudawa.
Kakakin magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya soki matakin da Tel Aviv ta dauka a matsayin siyasa da kuma tozarta dukkanin ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya.