Iran ta yi Allah-wadai da harin da Isra’ila ta kai kan jirgin ruwan da ke jigilar abinci zuwa Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani jirgin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani jirgin ruwa, da ke dauke da kayan abinci da na agaji zuwa zirin Gaza da ke gabar ruwan kasar Malta.

Esmaeil Baqaei ya yi tsakaci game da kisan kiyashin da ake yi a zirin Gaza, inda Ya ce, harin da aka kai kan jirgin ruwan mai dauke da kayan agaji, babban laifi ne, kuma ya zama ta’addanci.

Halin da ake ciki a Gaza ya kai intaha inda cikin sama da kwanaki 60, babu wani jirgin ruwa dauke da abinci, agajin jin kai, ko mai da ya isa zirin, lamarin da ya kara hadassa wahalhalu da tabarbarewar ayyukan jin kai a zirin wanda kuma ya shafi yara da iyalai da dama wadanda ke fuskantar yunwa.

Tun a ranar 7 ga Oktoba, 2023, Isra’ila ta fara kai farmaki Gaza, sannan lamarin ya tsanata bayan da Isra’ila ta yi fatali da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas.

Ya zuwa yanzu, sama da mutane 50,000 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai Zirin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments