Iran ta yi Allah-wadai da matakin da kungiyar G7 ta ke yi na nuna son kai da rashin da’a game da ci gaban da ake samu a yammacin Asiya, gami da matakin da Tehran ta dauka kan matakin wuce gona da iri na Isra’ila.
Shugabannin kungiyar G7 a cikin wata sanarwa a ranar Laraba sun yi Allah wadai da harba makamai masu linzami da Tehran ta yi kan Tel Aviv a matsayin ramuwar gayya kan kisan da Isra’ila ta yi wa shugabannin Hamas da Hizbullah da wani kwamandan sojojin Iran.
Sabon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baqaee Ya yi gargadi game da mummunar illar da wannan hanya za ta haifar ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Baqaee ya ce: Harin makami mai linzami na baya-bayan nan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai kan cibiyoyin sojojin yahudawan sahyoniyawan da na leken asirinsu, wani martani ne da ya wajaba kan ayyukan wuce gona da iri na gwamnatin mamaya.
Kakakin ya ce, aikin yana cikin tsarin hakkin kare kai, yana mai yin Allah wadai da amfani da barazana da takunkumin da ake yi na matsin lamba ga al’ummar Iran.
Baqaee ya jaddada aniyar Iran na kare tsaron kasarta da kuma muhimman muradun al’ummar Iran a yankin.
Har ila yau, ya soki lamirin “shisshigin kasashen, ciki har da Amurka, musamman ta hanyar ci gaba da goyon bayansu ga gwamnatin mamayar Isra’ila” wanda ya bayyana a matsayin “babban dalilin rashin zaman lafiya a yankin yammacin Asiya”.
“Idan har da gaske ne kungiyar ta G7 ta damu da zaman lafiya da tsaro a yankin, to ya kamata ta yi amfani da karfin da take da shi wajen kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke wa Falasdinawan da kuma dakatar da wuce gona da iri ke yi kan kasashen Labanon, Siriya da sauran kasashen yankin.”