A zantawa ta wayar tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin.
A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar.
Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a kasashen yankin, ya kuma bayyana muhimmancin mutunta al-amuran da suka shafi cikin gida na ko wace kasa a yankin.
Sai kuma Hakan Fidan ministan harkokin wajen Turkiya wanda ya sake jadda matsayin kasarsa wajen neman hanyoyin diblomasiyya don warware matsalolin al-amuran Falasdinu da kasashen yankin da kuma sauran kasashen duniya.