Sayyid Ammar Hakim Shugaban jam’iyyar National wisdom yace martanin da Iran ta mayar kan harkin da Isra’ila ta kai mata a ofishin jakadancinta dake birnin Damaskas na kasar Siriya ta tabbatar da karfin ikonta a duniya.
Har ila yau a wani zama na kasa da kasa da aka gudanar a birnin sulaimaniya dake yankin kurdustan na kasar iraki, ya fadi cewa yayi Imani cewa babban hadafin da yasa iran take mayar da martani shi ne tabbatar da hakkinta na mayar da martani ne ba don haifar da rikici da rashin tsaron ba.
Daga karshe ya jaddada game da muhimmancin fitar da sojojin kasashen waje musamman kasar Amurka daga kasar Iraki ,yace dole ne a kawo karshen ci gaban da zaman sojojin kawance ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.