Iran, ta yi watsi da ikirarin baya-bayan nan na zargin hannu kasar a yunkurin kashe jami’an Amurka na da ko na yanzu
Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar y ace wannan zargin ba shi da tushe.
A cikin bayaninsa, Baghaei ya yi ishara da irin wadannan zarge-zarge da aka yi a baya, wadanda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi fatali da su da kakkausar murya, kuma daga baya aka tabbatar da cewa karya ce.
Ya bayyana hakan da wata mummunar makarkashiya da kungiyoyin yahudawan sahyoniya da masu adawa da Iran suka shirya da nufin kawo cikas ga alaka tsakanin Amurka da Iran.
A baya-bayan nan ne ma’aikatar shari’a ta Amurka ta shigar da karar Farhad Shakeri, wani dan kasar Afganistan, wanda ake zargin dakarun kare juyin juya hali na Iran da kitsa masa yunkurin kisan gillar da aka yi wa Donald Trump gabanin zaben shugaban kasa.