Iran Ta Musanta Zage-Zargen Kasashen Turai 3 Na Baya-Bayan Nan Kan Shirin Nukliyar Kasar

Gwamnatin Kasar Iran ta musanta zargin kasashen Turai uku wato E3 na baya-bayan nan, sannan ta kara da cewa zata maida martanin da ya dace

Gwamnatin Kasar Iran ta musanta zargin kasashen Turai uku wato E3 na baya-bayan nan, sannan ta kara da cewa zata maida martanin da ya dace a wannan rigimar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esma’il Baghae kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadara haka a maida martani ga kasashen Turan guda uku, wato Faransa, Jamus da kuma Burtaniya, wadanda suka bada sanarwan hadin giuwa kan cewa “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sabawa yarjeniyar JCPOA ta shekara 2015 wacce ta takaita mata mizanin makamashin Uranium da zata tace, kamar yadda kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 ta zayyana”.

Baghaie ya kara da cewa Iran ta sabawa yarjeniyar JCPOA ne bayan da Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018, sannan ta dora mata takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar. Sannan kasashen na turai suka kasa cika alkawalin da suka dawkawa Iran a wannan bangaren.

A ranakun 14-15 ga watan Nuwamban da ya gabata ne wadannan kasashe 3 na Turai suka jagoranci wasu gwamnonin hukumar IAEA suka yi allawadai da JMI kan abinda suka kira rashin bada hadin kai ga hukumar ta IAEA a cikinta na makamshin Nukliya.

Don haka Iran tare da amfani da hakkinta na mallakar fasahar nukliya ta zaman lafiya ta maida martani da tace makamashin yuranium fiye da yadda yarjeniyar JCPOA ta yerje mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments