Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu.
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da babban sakataren kungiyar kasashen larabawan yankin tekun pasha a birnin Muscat na kasar Oman a jiya Lahadi.
Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya kara da cewa; ya zama wajibi a ji sauti daya daga kasashen musulmi na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falasdinu.
Arakci wanda ya yi ishara da ganawa ta farko da aka yi a matakin ministocin kasashen kungiyar larabawa ta yankin tekun Pasha da kuma na Iran, Arakci ya jaddada muhimmanci cigaba da tattaunawa domin samar da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.
Ministan na harkokin wajen Iran din ya yaba wa kasashen laraabwa,musamman na yankin tekun Pasha dangane da matsayin da su ka dauka na kin amincewa da shirin Amurka da ‘yan sahayoniya na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza. Haka nan kuma ya yi tir da furuci na tsokana da ya fito daga bakin Benjamine Netanyahu akan cewa Saudiyya ta bai wa Falasdinawa yankin da za su kafa kasarsu a cikinta.
Arakci dai ya je Oman ne domin halartar taron kungiyar kasashen da suke iyaka da tekun Indiya da shi ne karo na 8. Taken taron dai shi ne Bunkasa sabbin hanyoyi aiki tare a doron ruwa a tsakanin kasashen.