A yau Lahadi ce ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran ta kira jakadan kasar Chaina a Tehran zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don bayyana korafinta kan yadda kasar ta Chaina ta bayyana amincewarra da zargin Iran da mamaye tsibirai guda uku mallakin UAE a cikin tekun Farisa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Chaina tare da UAE a wani taron da suka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata sun fidda jawabin bayan taro inda wannan zargin ya zo a sakin layi na 26 na jawabin bayan taron kasashen biyu. A cikin bayanin dai, kasar Chaina ta amince da ikrari na karya wanda UAE take yi na mallakar tsibirai guda uku a cikin tekun Farisa wadanda suke karkashin ikon Iran a halin yanzu.
Labarin ya kara da cewa JMI tana da hujjoji kwarara wadanda suke tabbatar da cewa tsibiran Abu Musa Tumbe Kucek da Tumbe Buzarg mallakin kasar Iran ne na daruruwan shekarun da suka gabata.
Jakadan kasar Chaina Cong Peiwu ya je gaban Muhammada Alibak matamakin ministan harkokin waje, sannan darakcta mai kula da kasashen yankin tekun farisa a ma’aikatar. Inda darectan ya bayyana masa korafi JMI dangane da abinda ya zo cikin jawabin bayan taro na kasashen 2.
Gwamnatin UAE ta sha bayyana cewa shibiran guda uku nata ne, kuma tana neman taimakon manya manyan kasashen duniya don kwato su daga hannun kasar Iran. A tarihi dai tsibiran sun kasashen karkashin mamayar turawan Burtania tun shekara ta 1921 har zuwa watan 30 ga Nuwamban shekara 1971, suka koma karshin ikon kasar Iran kawana guda bayan barin turawan wadannan wurare guda uku. Kuma kwanaki kafin samun yencin UAE.