Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan a zirin Gaza, yana mai kira da a kawo karshen kisan kiyashi da rashin hukunta shugabannin gwamnatin ‘yan shayoniyya da kuma gurfanar da su a gaban kuliya don hukunta su.
Baqa’i ya yi ishara da laifuffukan da ba a taba ganin irinsa ba da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi kan al’ummar Falastinu da ba su da kariya a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ya kuma yi kakkausar suka kan munanan hare-haren da aka kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira na wucin gadi da cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza, wanda ya yi sanadin shahada da jikkata daruruwan mutane a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata. Ya yi nuni da alhakin kai tsaye da ke wuyan masu kare gwamnatin ‘yan mamaya da magoya musu baya a fagen soja da na siyasa, musamman Amurka da Birtaniya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce: “A halin da ake ciki, bayan gaza cimma matsaya a yunkurin masu shiga tsakani na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ‘yan mamaya sun kara zafafa kai hare-haren ta’addanci da nufin gabatar da wasu bukatu da ba su dace ba, da kuma raba mazauna yankin Zirin Gaza da muhallinsu, wanda tabbas hakan zai fuskanci turjiya daga al’ummar Falasdinu.”