Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki.

Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba Putin ya isar da sakonsa ga JMI wanda kuma shi ne wai yana son warware matsalolin sa da JMI cikin lumana da zaman lafiya, ba tare da fito na fito ba.

Akwai jita-jita da dama a cikin yan kwanakin da suka gabata kan cewa HKI da Amurka a wannan karon har da kasashen yammam na shirin farwa kasar Iran da yaki da nufin lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar don hanata abinda suka kira makaman Nukliya.

Baghaei ya bayyana cewa JMI ta kare kanta daga hare-haren Amurka da kuma da kum HKI a cikin yakin kwanaki 12 da suka dora mata sannan a shirye take ta fuskance yaki wanda ya fi na watan yunin da ya gabata tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments