Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekunan Farisa Da Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya

Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar

Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban  jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar.

Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha  cikin yankin sama da wata gusa, sannan suna binsu suna kashewa.

Majiyar dakarun IRGC ta bayyana cewa sama da jiragen ruwa da kwale-kwale kimani 3,000 ne suka fito don tallafawa falasdinawa musamman a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, wadanda sojojin yahudawa suka kashewa a ko wace rana.

Labarin ya kara da cewa, a kudancin kasar an baje kolin katafaren jirgin ruwa mai daukar jirage yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, mai sun a ‘shahida beheshti’, jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa suna sauka su kuma tashi a kan wannan jirgin yakin.

HKI dai wacce take samun tallafin kasashen yamma musamman Amurka suna mamaye da kasar Falasdinu fiye da shekaru 70 a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments