Iran Ta Gargadi Kasashen Duniya Dangane Da Hatsarin Da Ke Tattare da Hare Haren HKI Kan Ofishin Jakadancinta A Siriya

Jakadan kuma matamakiyar jakadan JMI a MDD, bayan ta yi allawadai da hare haren da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin JMI a birnin

Jakadan kuma matamakiyar jakadan JMI a MDD, bayan ta yi allawadai da hare haren da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin JMI a birnin Damascus na kasar Siriya ta kara da cewa sakon da wadannan hare hare suke isarwa ga kasashen duniya yana da matukar hatsari.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Zahra Ershadi tana fadar haka a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya Talata, inda kwamitin yake gudanar da taro na musamman kan wadannan hare hare.

Ershadi ta kara da cewa HKI tana son yada yakin da ta kunna a cikin kasar Falasdinu da ta mamaye da kuma kasashen da suke makobtaka da ita.

Banda haka tana son yakin ya wasu zuwa sauran kasashen yankin kudancin Asiya wanda kuma ba alkhairi ne ga kasashen yankin da kuma duniya ba.

Mataimakiyar jakadan ta kara da cewa hare haren da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin JMI a birnin Damascus na kasar Siriya sun keta manya manyan kudurin MDD na keta hurumin kasashen duniya musamman Siriya da JMI.

Har’ila yau sun keta kudurorin Majalisar wadanda suka hada da na 1961, 1963 da kuma na 1973. Wadanda suke tabbatarwa ko wace kasa yencin da mutuncin jami’an diblomasiyyar ko wace kasa a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments