Iran Ta Gargadi Amurka Kan Shiga Cikin Al-Amarin Hare Haren Da Ta Kaiwa HKI A Jiya Da Dare

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da shishigi a cikin hare haren maida martanin da ta kaiwa HKI a

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da shishigi a cikin hare haren maida martanin da ta kaiwa HKI a jiya Talata. Sannan ya kara da cewa duk wani maida martanin da HKI da kawayenta zasu yi zai gamu da wani maida martani mafi tsanani.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a wata hira da ya yi da talabijin ta cikin gida a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa hare haren jiya sun samu kashi 90% na bararsu a HKI.

Ministan yana maida martani ne ga kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka wanda ya bayyana cewa Amurka tana goyon bayan HKI ido a rufe.

Matthew Miller ya fadawa kafafen yada labaran Amurka kan cewa Amurka tana goyon bayan HKI da kuma mutanen kasar a cikin wannan mummunan halin da suka fada ciki.

Hare haren kasar Iran wanda aka yiwa suna ‘Wa’adin Gaskiya Na 2″ an kaisu ne don maida martani kan kissan da HKI ta yi wa Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas da Sayyid Hassan Nasarralla shugaban kungiyar Hizbullah da kuma Abbas Nilforoushan, wani babban Jamai’in soje a rundunar IRGC ne

Daga karshe Abbas Aragchi ya bayyana cewa: bayan hare haren ‘waadussadiq 2- Iran ta aikewa Amurka sakon gargadi  ta ofishin jakadancin Swizland da ke birnin Tehran, saboda itace take wakiltan Amurka a Tehran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments