Ministan Harkokin Wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gargadi Amurka da Isra’ila game da goyon bayan da suke bai wa masu zanga-zangar, matsin tattalin arziki a fadin Iran zuwa tashin hankali.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa ranar Asabar a shafin ”X”.
Kafin hakan dama Rundunar Sojin Iran ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi gargadi game da makircin kasashen waje sanadin tarzomar da ake yi kwanan nan a birane da dama a fadin kasar, tare da yin kira ga ‘yan kasar da su kasance masu taka tsantsan game da makircin kasashen waje na neman haifar da tashin hankali a kasar.
“Rundunar sojin Iran ta yi kira ga ‘yan kasar Iran dasuyi taka tsantsan da kuma sanin yakamata da su kasance cikin shiri da kuma amfani da hankali don dakile makircin abokan gaba, da kuma kiyaye hadin kan kasa da hadin kai don hana abokan gaba cimma burinsu na mugunta,” in ji sanarwar da rundinar sojin iran ta fitar a ranar Asabar.