Mataimakin shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ya bada sanarwan cewa tuni hukumarsa ta kara karfin tace makamacin Yuranium a daya daga cikin cibiyoyin tace shi a yau Jumma’a, saboda maida martani ga gwamnonin hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA, wadanda suka yi tir da kasar a shirinta na makamashin nukliya a taronsu na jiya Alhamis.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Behrousz Kamalvandi yana fadar haka ya kuma kara da cewa a cikin ziyarar da shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi ya kawo nan Iran a cikin yan kwanakin da suka gabata, an je da shi zuwa cibiyoyin tace makamashin yuranium har guda biyu a kasar, kuma an nuna masa cewa matukar gwamomin hukumarsa sun yi tir da kasar Iran a taronsu na ranar Alhamis, to kuwa zasu maida martani da kara karfin tace makamacin Yuranium a cibiyar tacewa da ke Fordow.
Ya ce sun nunawa Rafael Gorossi injunan tace makamacin Yuranium sabbi wadanda ke jirin sakamakon taron gwamnoninsa.
Kamalvandi ya bayyana cewa kasashen yamma suna kuskure dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kuma da alamun zasu ci gaba da wannan kuskuren na gaba. Yace: yakamata gwamnonin su san cewa hanyar da suka dauka ba zata taba maida shirin makamashin nukliya na kasar Iran baya ba.
Don haka iran zata kara fadada shirinta na bincike na kuma ilmi don gano sabbin abubuwan da suka shafi nukliya don amfanin mutanen kasar. A halin yanzu dai Iran tana tace makamacin yuranium har zuwa kashi 60%.