Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran a shirye take ta maida martani ga duk wata barazana ga shirinta na makamashin nukliya, amma kuma a dayan bangaren tana aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta Duniya (IAEA).
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka, a zantawarsa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya Rafael Grossi.
Ministan ya aibata wasu gwanonin hukumar ta IAEA kan matakan da suka dauka kan Iran a taronsu na fasalin da ya gabata, wato na watan Nuwamban wannan shekarar. Ya ce wannan ya sa gwamnatin kasar Iran ta dauki matakan maida martani a kan hukumar. Inda ta sauya na’urorin centrifution da take amfani da su a da, wajen tace makamashin Uranium zuwa wasu sabbi, kuma wadanda suka fi na farkon karfi.
Ya ce kasar Iran a shirye take ta sake komawa teburin tattaunawa da hukumar don warware sauran al-amuran da suka rage, ta ke sabani a kansu da hukumar.
Kafin haka dai babban sakaren hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya ziyarci cibiyoyin tace makamashin Uranium na Natanz da Fordow a cikin watan Nuwamban da ya gabata kafin taron gwamnonin hukumar.
Kasashen Burtaniya, Faransa da kuma Jamus ne suka gabatar da korafi dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran a gaban gwamnonin hukumar, inda suka bukaci rahoton na musamman kan shirin Nukliyar kasar ta Iran.