Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Matsayin Amurka a cikin ɗakin tattaunawa da Iran ya bambanta da abin da suke shelantawa a waje
Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Kalamai da matsayar da jami’an Amurka suka dauka a cikin dakin tattaunawa da Iran suna shan bamban a fili da abin da suke bayyanawa a bainar jama’a, yana mai cewa wannan sabani yana dakushe kwarin gwiwar bangaren Iran da kuma yin barazana ga makomar shawarwarin.
A wata hira da ya yi da mujallar Der Spiegel ta Jamus, Takht-Ravanchi ya bayyana kin amincewar da Iran ta yi da bukatar “samar da sifili na Uranium da take sarrafawa”, yana mai jaddada cewa inganta sinadarin Uranium don manufar zaman lafiya wani muhimmin bangare ne na shirin makamashin nukiliyar Iran kuma wani hakki ne da ba za a iya tattaunawa kansa ba.
Yana mai jaddada cewa: “Idan har Amurka ta nace da batun dakatar da duk wani abu da ake yi na inganta sinadarin Uranium, to lallai tattaunawar da ake yi ba za ta kai ga gaci ba,” Ya kara da cewa: Tace sinadarin Uranium wani babban nasara ce ta kasa, kuma Iran ba za ta yi watsi da shi ba, yana mai jaddada cewa har yanzu ba a sanya batun wa’adin (kamar shekaru 25) kan teburin tattaunawa ba.