Kakakin gwamnatin Iran Ali Bahadori Jahromi ya caccaki ‘yan majalisar dokokin Amurka kan baiwa jami’an Isra’ila kariya, a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa kotun hukunta manyan laifuka ta ICC na shirin bayar da sammacin kame mambobin gwamnatin Isra’ila ciki har da Firaminista Benjamin Netanyahu kan yakin da Isra’ila ke yi a yankin Zirin Gaza.
Bahadori ya yi nuni da cewa a ranar Juma’a wasu kasashen yammacin duniya sun keta dokokin kasa da kasa karara.
Ya kara da cewa matakin son zuciya da kasashen yammacin duniya ke dauka ya kawo cikas ga ci gaba da aiwatar da tasiri na dokokin kasa da kasa.
Kakakin na Iran ya kara da cewa, kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi kan mata da kananan yara, da hare-haren da take kaiwa kan gidajen jama’a, cibiyoyin kiwon lafiya, da ma sansanonin Majalisar Dinkin Duniya a cikin watanni 7 da suka gabata, ya bayyana hakikanin matsayin wasu kasashen yammacin duniya kan batun kare hakkin bil’adama.
Bahadori Jahromi ya jaddada cewa, wadannan ayyuka suna nuna rashin tasirin dokokin kasa da kasa wajen hana irin wannan ta’asa.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da kafar yada labarai ta Axios ta Amurka ta bayyana cewa, ‘yan majalisar wakilai na Republican suna tsara wani kudirin doka da nufin kakabawa jami’an ICC takunkumi a matsayin martani ga yiwuwar fitar da sammacin kama jami’an Isra’ila kan laifukan yaki a Gaza.