Iran Ta Bukaci Kasashen Turai Su Dakatar Da Taimakon Da Suke Bawa HKI A Kissan Kare Dangin Da Take Aikatawa A Gaza

Ofishin jakadancin JMI dake kasar Island ta bukaci kasashen turai su dakatar da taimakon da suke bawa gwamnatin HKI saboda kissan kare dangin da take

Ofishin jakadancin JMI dake kasar Island ta bukaci kasashen turai su dakatar da taimakon da suke bawa gwamnatin HKI saboda kissan kare dangin da take yi a kan al-ummar Falasdinu a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na daliban Jami’a a nan Iran ya nakalto ofishin jakadancin JMI a yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa yakamata kasashen su dai kariya su dawo daga rakiyar Benyamin Natanyahu a kissan kiyashin da yake yi a Gaza.

A wani bangare kuma Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bayyana cewa yana kan bakansa na kai farmaki kan garin Rafah dake kudancin Zirin gaza inda falasdinawa yan gudun hijira kimani miliyon 1.5 suke samun mafaka tun bayan fara yakin Tufanul Aksa watanni fiye da 6 da suka gabata.

Manufar HKI na korar Falasdinawa daga arewaci da tsakiyar gaza zuwa garin Rafah na kan iyakar kasar Masar da HKI dai itace, korar Falasdinawa daga kasar Falasdinu zuwa cikin yankin Sina na kasar Masar.

Ya zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kasha Falasdinawa fiye da  34,000 a gaza mafi yawansu mata da yara. Kuma tana ci gaba da kisa har yanzun da muke bada wannan labarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments