Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda Jami’an diblomasiyyar kasar a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Yuli n shekara 1982.
Jami’an diblomasiyyar suna ne Seyed Mohsen Mousavi, Ahmad Motevaselian, Kazem Akhavan, and Taghi Rastegar Moghadam, wadanda wata kungiyar yar ta’adda wacce HKI take goyon bayanta ta kamasu ta kuma mikawa HKI a lokacinda take mamayae da kasar Lebanon.
Rahoton ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon kan hadin kan da take bayarwa don ganin wadan nan Jami’an diblomasiyya sun koma cikin iyalansu.
Ya ce: Yin garkuwa da Jami’an diblomasiyya ya sabawa dokar Vienna ta shekara 1961 da ya shafi jami’an diblomasiyya ya kuma sabawa doka ta garkuwa da mutane ta shekara 1979.