Iran ta bukaci a kakaba wa Isra’ila takunkumi kan kisan kiyashin Gaza

Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin

Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan.

Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60 a birnin Geneva, wakilin kasar Iran Ali Bahreini ya yi ishara da rahoton da kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan yankin Falasdinu da ta mamaye a watan Satumba, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a zirin Gaza.

Hukumar, wacce ke binciken abubuwan da suka faru tun ranar 7 ga Oktoba 2023, ta gano cewa hukumomin Isra’ila da jami’an tsaronta sun aikata hudu daga cikin ayyukan kisan kare dangi biyar da yarjejeniyar kisan kare dangi ta 1948 ta ayyana.

Wadannan sun hada da kisa, da azabtarwa da gangan ta da nufin halaka al’ummar Falasdinu gabaki daya.

Jami’in na Iran Ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da kasashen yammacin duniya ke yi, ko na siyasa, ko soja, ko na tattalin arziki ko kuma na daban ga Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted