Iran Ta Bayyana Muhimmancin Kasar A Hada Kasashen Turai Da Asia Ta Gabas Da Yamma Da Layin Dogo

A taron kasashen kungiyar ‘Shanghai Cooperation Organization (SCO)’ karo na 5TH da ke gudana a birnin Mosco na kasar Rasha, ministan sifiri kuma shugaban kamfanin

A taron kasashen kungiyar ‘Shanghai Cooperation Organization (SCO)’ karo na 5TH da ke gudana a birnin Mosco na kasar Rasha, ministan sifiri kuma shugaban kamfanin jiragen kasa na kasar Iran, Jabarali Zakeri ya bayyana yadda kasar Iran ta zama kasa wacce take iya hada nahiyar Turai da kuma kasashen Asiya ta gabas da yamma tare da layin dogo.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron shuwagabannin kamfanonin jiragen kasa na kungiyar SCO karo na 5TH  wanda ke gudana a halin yanzi a birnin Mosco. Ya kuma kara da cewa yanayin da kasar Iran take a yankin Asia ya bata damar samar da hanyar zirga-zirgan jiragen kasa mafi sauki tsakanin Nahiyar Turai zuwa kasashen Asiya ta gabas da yamma. Tare da hadin kan kasashe uku, a yankin, wato Iran, Rasha da Azerbaijan.

Tare da hadin kan wadannan kasashe uku, dukka kasashen Turai suna iya amfani da layin dogo don isa zuwa mafi yawan kasashen Asiya ta gabas da ta yamma a cikin karamin lokaci da kuma farashi mai rahusa.

A halin yanzu dai ayyukan da aka gabatarwa don tabbatar da wannan shirin suna dab da kammala.

Banda haka, idan an kammala wannan shirin, jiragen kasa wadanda zasu ratsa ta kasar Iran, suna iya daukar kayaki da mutane daga Tekun Caspian daga arewacin kasar Iran zuwa tekun Farisa na kudancin kasar daga jiragen ruwn da zasu saukesu a wadanan tekuna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments