Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghae ya zargin gwamnatin Amurka da yin ba daidai ba saboda karin takunkuman tattalin arziki wanda ta dorawa kasar, wanda kuma yake nuna irin kiyayyar da takewa mutanen kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esmael Baghae yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa bayan da hukumar baitul malin Amurka ta bayyana sunayen mutane 10 wadanda ta dorawa takunkuman tattalin arziki da kuma kamfanoni 27 mafi yawansu a hadaddiyar daulolin larabawa wato UAE.
Labarin ya kara da cewa wadan nan mutane suna taimakawa Iran a ayyukan Banki da jigilar manfetur a madadin Iraniyawa. Baghae ya bayyana wannan labarin a kan kariya kuma mummunan siyasar Amurka ce ga JMI.
Yace bayan haka wadan nan takunkuman basa bisa ka’idar doka kuma manufa it ace takurawa mutanen kasar Iran.
Sannan ya kammala da cewa wadan nan matakan zasu kara karfafa dauriyan mutanen kasar Iran ne kawai. Inji Baghe.
Sannan abin mamaki shi ne wadannan takunkuman suna zuwa ne a dai-dai lokacinda kasashen biyu suke tattaunawa kan shirin makamashin Nukliya na kasar. Wanda ya nuna cewa Amurka bata nufin alkhairi a tattaunawar.