Binciken karshe da sojojin Iran suka gudanar kan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi ajalin tsohon shugaban kasar Ibrahim Raeisi da wasu mukarabansa, ya nuna cewa rashin kyawan yanayi da ya hada da mummunan tirnikewar hazo ne silan hatsarin jirgin.
Jirgin mai saukar ungulu dauke da Shahid Ra’isi da tsohon ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da wasu mutane 6 ya fadi ne cikin tsaunuka a ranar 19 ga watan Mayu a arewa maso yammacin kasar Iran.
Rahoton wanda babban hafsan sojojin kasar Iran ya wallafa a ranar Lahadi, ya kawo karshen jita-jitar yin zagon kasa ko kuma kawo cikas a matsayin musabbabin aukuwar wannan mummunan lamari, yana mai cewa tirnikewar yazo da rashin kyawon yanayin yankin a lokacin ne babban abin da ya haddasa hadarin jirgin. .”
Ya kara da cewa “fitowar hazo ba zato ba tsammani” ya sa jirgin helikwafta ya fado a gefen tsaunuka.
Rahoton ya ce, duk wasu takardu da suka shafi gyaran jirgin da kuma kula da shi tun lokacin da aka sayo shi da kuma amfani da shi kafin faruwar lamarin, kwararrun sojoji da na farar hula sun yi nazari sosai, inda suka sanar da cewa an gudanar da dukkan matakan ne bisa ka’ida.