Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar ta kasar Iran.
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran za su fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku.
Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne mu kara karfinmu na yaki, inji sakataren tsron na Amurka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, kalaman da jami’in na Amurka ya yi suna haifar da sabani da kuma yada abin kasar Sin ke kallonsa a matsayin barazana ga kasarta.
Lin ya kara da cewa, “Muna kira ga Amurka da ta daina gina tunaninta akan masaniyarta dangane da Sin a lokutan baya, musamman lokacin yakin cacar baki, domin kuwa a yanzu Sin ba wadda Amurka ta san ice a lokutan baya ba.
Sakataren tsaron Amurka ya fada a wata hira da kafar yada labarai ta Fox News a ranar Larabar da ta gabata cewa, Amurka ta shirya tsaf domin shiga kowane irin yaki a duniya.