Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa kasarsa ko kdan, bata son fafada yakin da ke faruwa a yankin.
Kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar iran ya nakalto Abdullahiyan yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Austria, Alexander Schallenberg a jiya Litinin.
Ya kuma bayyana masa kan cewa hare haren maida martini wanda sojojin Iran suka kai kan HKI a ranar Lahadi, suna bias doka ta kare kai ne wanda doka ta 51 ta MDD ta amince da haka.
Abdullahiyan ya kara da cewa, abinda yake jawo Karin rikici a gabas ta tsakiya shi ne yakin da HKI take fafatawa da Falasdinwa a Gaza da kuma yankin yamma da kogion Jordan.
A na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Austria ya bayyana cewa tashe tashen hankula a yankin Asia ta kudu, zai cutar da kowa ne. Kuma Iran tana da hakkin maida martini kan hare haren da HKI ta kai kan ofishin jakadancnta a birnin Damascus na kasar Siriya.