Iran: Kotu Ta Yanke Hukuncin Tara Ta Dalar Amurka Biliyon Guda Kan Gwamnatin Amurka Saboda Goyon Bayan Laifuffukan Gwamnatin Sha Kan Mutanen Kasar

Wato kotu a nan Tehran ta yanke hukuncin tarar dalar Amurka biliyon guda kan gwamnatin Amurka saboda goyon bayan hukumar liken asiri ta gwamnatin Sarki

Wato kotu a nan Tehran ta yanke hukuncin tarar dalar Amurka biliyon guda kan gwamnatin Amurka saboda goyon bayan hukumar liken asiri ta gwamnatin Sarki Sha wato SAVAK a azabtar da mutanen kasar da tayi shekaru fiye da 45 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar shari’ar kasar na bada wannan sanarwan, a yau Lahadi. Ta kuma kara da cewa koto mai lamaba 55 a nan Tehran ta yanke hukuncin tarar dalar Amurka fiye da biliyon guda kan gwamnatin Amurka ne, saboda irin goyon bayan da gwamnatin Amurka ta bayar wajen kada hukumar SAVAK wace ta azabatar da Iraniyawa da dama kafin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.

Kafin haka dai mutane 15 ne daga cikin wadanda hukumar SAVAK ta azabtar suka shigar da kari a gaban kotu mai lamba 55, wacce aka kebe don sauraron shari’o’in kasa da kasa, inda suka bukaci diya don jinya da sayan magunduna, har’ila yau da diyar barnan dukiypyo da mummunan halin da hukumar ta yiwa mutanen kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments