Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya 

Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro

Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi.

A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma yi kira ga Washington da ta daina keta ikon kasar Venezuela a karkashin hujjar yaki da miyagun kwayoyi, sannan ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da Sakatare Janar António Guterres da su sauke nauyin da ke kansu na hana duk wani karin tashin hankali.

Amurka ta kai hare-hare akalla sau 20 kan kananen jiragen ruwa da take zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi a yankin Caribbean da Pacific, Wadannan sukayi sanadiyyar mutuwar mutane 80.

Tun daga watan Agusta, Amurka ta tura jiragen ruwa a yankin ciki har da katafaren jirin nan na sojojin ruwan ta mafi girma a duniya USS Gerald R. Ford da jiragen yaki samfarin F35 da dubban sojoji zuwa yankin Caribbean, bisa fakewa da yaki da kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi na Latin Amurka.

Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya yi watsi da zargin hannu a safarar miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa Washington tana amfani da batun don ci gaba da shirinta na “canjin gwamnati” da kuma kwace arzikin mai na Venezuela.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted