A Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar ne Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai ja sallar Juma’a a yau.
Zai kuma gabatar da wani muhimmin jawabi dangane da halin da ake ciki a Lebanon, Gaza da kuma yankin.
A halin da ake ciki dai jami’an Iran, na masu ci gaba da maimaita gargadin da aka yi wa Isra’ila da Amurka kan gigin mayar da martani kan harin makamai masu linzami na ranar Talata.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce Amurka na tattaunawa da Isra’ila game da matakin da gwamnatin yahudawan ke dauka.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya mika sako ga Amurka ta hanyar ofishin jekadancin Switzerland a Tehran inda ta gargade ta cewa “kada ta shiga yakin.”
Ya yi gargadi cewa”duk wata ƙasa da ta taimakawa Isra’ila ko ta bari aka yi amfani da sararin samaniyarta domin kai wa Iran hari, yana nuna ita ma za a iya kai mata hari.