Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da irin gagarumin aikin da sojojin kasar suka yi wajen kaddamar da harin makamai masu linzami a yankin Tel Aviv, yana mai cewa hakan ya kasance martani halastacce kuma bisa ka’ida da doka.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar Juma’a a yayin sallar Juma’a wadda ya jagoranta a babban masallacin Imam Khumaini da ke tsakiyar birnin Tehran.
Sallar ta biyo bayan taron addu’a ga shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a Beirut.
Ayatullah Khamenei ya siffanta Nasrallah “Dan’uwana, abin kauna kuma abin alfaharina, fuskar duniyar Musulunci da ake so, kuma harshe na al’ummomin wannan yanki.
Jagoran ya ce “Na ga ya wajaba na jinjina wa Sayyid Hasan Nasrallah (Allah Ya jikansa da rahama) a sallar Juma’a a birnin Tehran, da kuma isar da wasu sakonni ga kowa.”
“Dukkanmu muna bakin ciki da alhinin shahadar Sayyed. Wannan babban rashi ne kuma muna cikin bakin ciki matuka, amma zaman makoki ba yana nufin bakin ciki da damuwa da yanke kauna ba ne.