Iran: Jagora Ya Kada Kuri’arsa A Zaben shugaban Kasa Zagaye Na biyu, Kuma Ya Kodaitar Da Mutane Su Fito Don Kada Kuri’unsu

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyuul Khaminae, ya fito da sanyin  safiyar yau Jumma’a inda ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyuul Khaminae, ya fito da sanyin  safiyar yau Jumma’a inda ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a nan kasar Iran, don fidda shugaban kasa tsakanin yan takara biyu da suka rage wato Sa’id Jalili da kuma Masud Pezeskiyan.

Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bayanin yadda ya ga wasu suke Magana kan cewa mutane masu zabe zasu fito don kada kuri’unsu fiye da zabe zagaye na farko.

Jagoran ya kara da cewa, idan haka ne to yana da kyau, don zaben shugaban kasa shi ne zabe mafi muhimmanci a kasar Iran, kuma akwai bukatar mutane su fito don ganin sun bada gudumawarsu a cikin al-amarin siyasa mafi muhimmanci a kasar.

A zaben  shugaban kasa zagaye na farko, a kuma ranar jumma’ar da ta gabata,  masu kada kuri’a miliyon 24 ne suka kada kuri’unsu, daga cikin miliyon 61 da suka cancanci kada kuri’unsu. wannan kuma shi ne kasha 40% na wadanda suka cancanci kada kuri’in nasu.

A gobe Asabar ce  ake sanar ma’aikatar cikin gida na kasar Iran zata shelanta sunan wanda ya lashe  zaben shugaban kasa karo na 14 a kasar Iran,  kuma wanda zai maye gurbin marigayi shugaba Ibrahim Ra’isi, wanda ya rasa ransa a ranare 19 ga watan mayun da ya gabata a wani hatsarin jirgin sama a lardin Azabaijan ta gabas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments