Iran: HKI Zata Jefa Kanta Cikin Jahannama Idan Fa Farwa Kasar Lebanon Da Cikekken Yaki

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa hki zata jefa kanta cikin jahannama idan ta fadada yakin da take fafatawa

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa hki zata jefa kanta cikin jahannama idan ta fadada yakin da take fafatawa da kungiyar Hizabullah zuwa dukkan kasar ta Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Laraba bayan taron majalisar ministoci a nan Tehran.

Kani ya kuma kara da cewa gwamnatin HKI tana son yin dabarbaru don magance wasu matsalolin da take fama da su tun lokacinda ta fara yaki a Gaza a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023. Ya kuma kara da cewa kungiyar Hizbullah ta shiga yakin Tufanul Aksa ne don tallafawa Falasdinawan da suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza.

Kuma gwamnatin HKI ta san irin gagarumin rawar da kungiyar take takawa wajen tallafawa Gaza, don haka idan ta kuskara ta bude cikken yaki da kungiyar ko kuma da kasar Lebanon, to kuwa yakinta da Hizbulla zai game dukkan HKI.

A halin yanzu dai gwamnatin HK ta kasa cimmanu manufofinta na shiga yaki a gaza, wadanda kuma suka hada da shafe kungiyar Hamas daga doronkasa, dawo da fursinonin ta kimani 120 wadanda suke tsare a hannun kungiyar da kuma kwace zirin gaza gaba dayansa daga kungiyar Hamas.

Ya zuwa yanzu dai, kimani watanni 9 da fara yakin, sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 38,000 a yayimda wasu 87 000 suka ji Rauni. Sannan wasu rahotanni sun bayyana cewa mafi yawan Falasdinawa a gaza sun rasa gidajensu a cikin wannan lokacin, sannan sojojin yahudawan sun hana shigo da abinci ko ta ina wanda ya sa yunwa ta kashe kuma ci gaba da kashe mutane musamman yara kanana a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments