Iran: Isra’ila Na Son Jefa Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Rikici Mai Hatsari

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ja kunnen kasashen yamma dangane da goyon bayan da ba iyaka da suke bawa HKI. Jaridar Tehran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ja kunnen kasashen yamma dangane da goyon bayan da ba iyaka da suke bawa HKI.

Jaridar Tehran Times ta kasar Iran ta nakalto Abbas Argchi yana fadar haka a wani sako da ya aika a shafinsa na X, inda ya ka ra cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da wadanda suke tare da shi suna son jefa yankin gabas ta tsakiya zuwa cikin yaki mai hatsari a yankin.

Ya kuma kara da cewa fadada aikin sojen da gwamnatin Natanyahu ta yi daga gaza zuwa yankin yamma da kogin Jordan wani mataki mai hatsari ne wanda zai iya fadada yakin zuwa yankin gaba daya.

Ministan ya ce: Idan kasashen yamma basu dakatar da goyon bayan da suke bawa HKI a wannan yakin ba, to kuwa su ma suna daga cikin wadanda za’a tuhuma da laifukan yaki, ko ba dade ko ba jima sai an hukuntasu akan wannan laifin. Don tare da makamansu ne da kuma goyon bayansu, na siyasa ne Natanyahu yake aikata abinda yake yi a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin HKI suke loguden wuta a kan mutanen Gaza, inda ya zuwa yanzu sun kashe falasdinawa kimani dubu 42 sannan wasu dubu 93 suka ji rauni, mafi yawansu mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments