Iran: Hanya Daya Tilo Ta Sake Farfado Da Yarjeniyar JCPOA Ita Ce Tattaunawa

Jakadan kasar Iran kuma wakilin din din din na kasar a MDD ya bayyana cewa, barazana, ko yaki basu taba warware matsalar farfado da yarjeniyar

Jakadan kasar Iran kuma wakilin din din din na kasar a MDD ya bayyana cewa, barazana, ko yaki basu taba warware matsalar farfado da yarjeniyar JCPOA nashirin Nukliyar kasar Iranba. Hanya guda tilo ta farfado da ita shi tattauna a tasakanin kasashen da abin ya shafa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Amir Saeed Irawani yana fadar haka a wani taro na musamman a kwamitin tsaro na majalisar, inda aka tattauna dangane ‘naha amfani da makaman nukliya, da kuma yadda za’a aiwatar da kudurin majalisar mail amba 2231 wanda yake goyon bayan yarjeniyar JCPOA da yadda za’a aiwatar da ita’.

Iravani ya kara da cewa ya kara jadda matsayin JMI na nisantar makaman Nukliya, sannan hakkinta na amfani da makamashin nukliya ta zaman lafiya. Banda haka a shirye taka ta shiga tattaunawa da wadanda abin ya shafa don gonin an farfado da yarjeniyar.

Jakadan ya ce yarjeniyar JCPOA yana da matukar muhimmanci, kuma samuwarsa zai taimaka don kaucewa matsaloli dangane da shirin nukliyar Kasar Iran. Kuma har yanzun wannan yarjeniyar ita ce zabi mafi inganci don warware wannan matsalar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments