Majalisar dokokin kasar Iran ta kammala aikin tantance ministocin wadanda shugaba Pezeskiyan ya aika masu a makon da ya gabata don tantance su.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Augustan da muke ciki ne, wato kwanaki 12 da rantsarda shi a matsayin shugaban kasa, Masoud Pezeskiyan ya mika sunayen mutane 19 ga majalisar dokokin kasar don tantancewa a matsayin majalisar ministocinsa.
Labarin ya kara da cewa a ranar Lahadin da ta gabata ce majalisar ta fara tantance ministocin, sannan a cikin kwanaki kadan majalisar ta kammala aikin gaba daya ta kuma amince da dukkan ministocin da ya zama.
Kafin haka shugaban ya gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin a ranar Laraba inda ya tabbatar masu cewa bai yi wani kuskre a zabensu su ba
Kwamitoci daban daban a majalisar sun zauna da ministocin inda da farko suka dubi tarihiyan rayuwar kowanne daga cikinsu, sannan suka dubi takardun ilminsu sannan suka yi masu tambayoyi dangane da shirye shiryensu a ma’aikatun da aka basu.
Fitacce daga cikin ministocin dai shi ne Abbas Araqchi wanda ya maye gurbin marigayi Dr Hussain Amir Abdullahiyan a matsayin ministan harkokin wajen kasar.