Iran : Dole Ne Gwamnatin Syria Da Kungiyoyin ‘Yan Adawa Su Fara Tattaunawar Siyasa

Iran ta bayyana cewa dole ne gwamnatin Siriya da gungun masu dauke da makamai su fara tattaunawar siyasa. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi

Iran ta bayyana cewa dole ne gwamnatin Siriya da gungun masu dauke da makamai su fara tattaunawar siyasa.

Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya yi wannan kira bayan wata ganawa da ya yi da takwarorinsa na kasashen Rasha da Turkiyya a birnin Doha na Qatar yau Asabar.

Manyan jami’an diflomasiyyan kasashen uku dake tattaunawar samar da zaman lafiya a Siriya sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da ke faruwa a kasar bayan sake bullar gungun masu dauke da makamai a kasar ta Larabawa.

Ya ce batu “mafi mahimmanci” da bangarorin suka amince da shi shi ne cewa “a fara tattaunawa ta siyasa tsakanin gwamnatin Siriya da masu dauke makamai.”.

Ya kara da cewa ministocin harkokin wajen kasashen uku sun yi taro mai ma’ana, wanda kuma ya samu halartar manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Syria Geir Pedersen.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, an cimma matsaya a tsakanin dukkan mahalarta taron cewa, dole ne a kawo karshen tashin hankalin kasar Syria nan take, sannan kuma a mutunta hurumin kasar bisa kudurin MDD.

Ya kara da cewa, za a ci gaba da tuntubar gwamnatin Syria da sauran kasashe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments