Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bukaci a hukunta dukkanin jami’an siyasa da na soja na gwamnatin Isra’ila kan irin ta’asar da suka aikata.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a harshen yahudanci ta shafin X, a ranar Asabar.
“Dole ne a gurfanar da dukkan kyaftin din siyasa da na soji na kungiyar ‘yan ta’adda ta sahyoniya mai aikata laifi,” in ji sakon.
Kalaman na Ayatullah Khamenei sun zo ne bayan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta bayar da sammacin kame firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Yoav Gallant kan laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Duk da yaba hukuncin a matsayin “nasara,” Iran ta ce ya kamata a ce hukuncin ya hada da “kisan kare dangi” daga gwamnatin.