Iran Da Rasha Sun Rattaba Hannu Kan Cikakkiyar Yarjejjeniyar Manyan Tsare-tsare

Shugabannin kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare ta dogon lokaci. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da

Shugabannin kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare ta dogon lokaci.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Moscow.

Da yake magana a taron manema labarai na hadin gwiwa bayan kammala rattaba hannu kan yarjejeniyar, Pezeshkian ya ce yarjejeniyar za ta bude wani sabon babi na huldar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fagage, musamman a fannin tattalin arziki.

Ya ce duka Tehran da Moscow sun kuduri aniyar kawar da duk wani cikas ga harajin kwastam, bankuna, lamunin zuba jari, gudanar da tarurruka a tsakanin ‘yan kasuwa da kuma batun biza.

A nasa bangare Shugaban Rasha ya fifita fadada huldar kasuwanci da Iran, ya kuma ce a tattaunawar da suka yi da Pezeshkian, bangarorin biyu sun tattauna kan yadda za a kara mu’amalar kasuwanci.

Shugaban na Rasha ya kuma ce kasarsa da Iran suna adawa da matsin lamba daga ketare kuma suna ba da muhimmanci ga samar da zaman lafiya da tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments