Manyan hafsoshin sojin Iran da Pakistan sun kudiri anniyar yaki da ta’addanci domin inganta tsaron kan iyaka.
bangarorin sun ce kamata ya yi kasashen biyu su ci gaba da yaki da ta’addanci domin tabbatar da tsaro a yankunan kan iyakokinsu.
Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqeri, wanda ke birnin Islamabad a inda ya jagoranci wata babbar tawagar sojoji, ya gana da takwaransa na Pakistan, Janar Asim Munir, a yau Litinin.
Janar Baqeri ya ce kasashen biyu sun yi nasarar samu gagarumin ci gaba wajen tuntubar juna, musamman a fannin soji da na tsaro.
Ya kara da cewa, an daukai matakai masu “mahimmanci” na rufe kan iyakoki ta yadda za a iya yin zirga-zirga tsakanin kasashen biyu ta hanyar shige da fice na yau da kullun.
A nasa bangaren, babban hafsan sojin Pakistan ya ce, ya kamata kasashen yankin da suka hada da Iran da Pakistan su samar da hadin kai a wannan yanayi mai matukar muhimmanci.
Janar Munir ya kara da cewa Pakistan za ta dauki matakan da suka dace kuma cikin gaggawa don kawo karshen yunkurin ta’addanci a kan iyakokin kasar, yana mai jaddada cewa Tehran da Islamabad na neman fadada fahimtarsu a dukkan batutuwan da suka shafi hadin gwiwa.
Ya kuma yi suka kan rashin hadin kai tsakanin kasashen musulmi a yankin, ya kuma ce rashin hadin kai na al’ummar musulmi shi ya janyo kisan gilla da aka yi wa dubban Falasdinawa 50, da lalata gidajensu, da kuma raba dubunnan daruruwan jama’a da gidajensu a Gaza.