Iran Da Nijar Sun Sha Alwashin Karfafa Alakar Dake A Tsakaninsu

Kasashen Iran da kuma Jamhuriyar Nijar, sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a fagage da dama. Wannan bayyanin ya fito ne a yayin

Kasashen Iran da kuma Jamhuriyar Nijar, sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a fagage da dama.

Wannan bayyanin ya fito ne a yayin ganawar da sabon shugaban aksar Iran, Massoud Pezehskian, ya yi da wakili na musamman na shugaban kasar Nijar kana minsitan tsaron kasar, Janar Salifou Mody a birnin Tehran.

Janar Mody, ya mika sakon shugaban majalisar ceton kasa ta Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, ga zababen shugaban kasar ta Iran, tare da yi masa fatan alhairi da kuma nasara akan mukaminsa na shugabancin kasar ta Iran.

Shi dai wakilin na musamman na shugaban kasar ta Nijar, wato Janar Salifou Mody kana kuma minsitan tsaron kasar, da tawagarsa ciki har da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou, sun halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar ta Iran a ranar Talata.

A lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasar Iran, Mirigayi Shahid Ebrahim Ra’isi, kasashen biyu sun cimma yarjejeniyoyi da dama a tsakaninsu ta fuskar makamashi, kasuwanci tsaro da dai sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments