Manya-Manyan Jami’an gwamnatin kasar Iran da tokwarorinsu na kasashen turai uku wadanda ake kira, E3 zasu fara tattaunawa a tsakaninsu dangane da tattaunawa dangane da makamashin nukliya tsakanin Iran da Amurka wanda ke ci gaba a halin yanzu.
Kasashen E3 dai sun hhada da Faransa, Jamus da kuma Ingila wadanda suke sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu a shekara ta 2015. Manufar taron ko kuma tuntubar juna tsakanin Iran da wadannan kasashe uku itace sanyasu a kan hanya kan yadda tattaunawar take tafiya, da kuma yadda ake son a gabatar da sauye-sauye wa yarjeniyar JCPOA, tunda Amurka ta waresu daga wannan tattaunawar.
JMI tana ganin idan har an cimma wata yarjeniya da Amurka kan shirinta na makamashin nukliya ba zai bambanta sosai da JCPOA ba.
Yarjeniyar JCPOA sai ta shiga rudu tun bayan da shugaban Amurka mai ci ya fidda Amurka daga yarjeniyar a shekara ta 2018. Sannan kasashen Turai wadanda suka sanyawa yarjeniyar hannu a shekara ta 2015 suka biyewa Amurka suka dakatar da amfani da yarjeniyar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya tabbatar da hakan , ya kuma bayyana cewa za’a fara gudanar da taron a gobe Jumma’a 17 ga watan Mayu a birnin Istambul na kasar Turkiyya.