Jakadan kasar Iran kuma wakilinta na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya aike da wasika zuwa ga kwamitin sulhun Majalisar da babban sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya, inda ya yi la’akari da cewa, laifuffukan gwamnatin mamayar Isra’ila da ta yi wa kasar Lebanon babban cin zarafi ne ga ‘yancin kasar ta Lebanon da kuma amincin kasarta, don haka Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana bukatar kwamitin sulhun Majalisar da ya yi Allah wadai da wadannan munanan ayyukan laifuffuka da kuma daukar matakan masu tsauri na hukunta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Sakon wasikar Jakadan na Iran ga shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da babban sakataren Majalisar dangane da shahadar Masoumeh Karbasi da mijinta dan kasar Lebanon a yankin Jounieh mai yawan jama’a a birnin Beirut, da na Ali Heydari likitan kasar Iran ma’aikacin jinya a birnin Beirut, ta hanyar hare-haren wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya, ya bayyana cewa: Ta hanyar wannan wasiƙar, yana ja hankalin kwamitin sulhu da Majalisar Dinkin Duniya kan wannan babban abin kunya da ta’addanci da sahyoniyawan suka aiwatar. A wannan karon ‘yan sahayoniyya sun kai hari kan ‘yan kasar Iran a Lebanon, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa, musamman ma dokokin jin kai na kasa da kasa.